in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sojojin Sudan ta Kudu sun yi wa mata fyade
2015-06-30 19:48:48 cri
Tawagar wanzar da zaman lafiya dake Sudan ta Kudu ko UNMISS a takaice, ta ce, sojoji da dakaru masu dauke da makamai a Sudan ta Kudu sun yi wa mata fade tare da kona wasu da ran su.

Tawagar ta ce sassan dakarun kasar sun tafka ta'asa, tare da keta mutuncin bil'Adama. Ya kuma bada misali da yadda dakarun SPLA da na kawayen ta dake gundumar Mayom, suka rika farwa fararen hula a yankin.

An ce dakarun sun rika yiwa mata fyade, tare da wawashe dukiyoyin al'umma. Baya ga kuma kauyuka da dama da suka tarwatsa, lamarin da ya tilasawa kimanin mutane 100,000 tserewa daga gidajensu.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China