Cikin wata sanarwar da kakakinsa ya fitar, Mr. Ban ya yi kira ga daukacin masu ruwa da tsaki a rikicin kasar da su dakatar da bude wuta, tare da rungumar tafarkin wanzar da zaman lafiya, domin kawo karshen halin kunci da 'yan kasar ke fama da shi.
Sanarwar ta kuma rawaito Mr. Ban na yin Allah wadai, da kisan ma'aikatan wata kungiyar bada agajin jin kai mai zaman kanta su 5 a jihar Upper Nile. Lamarin da ya haddasa barkewar fada tsakanin dakarun sa kai masu ikirarin kare gundumar Maban, da sojojin da suka yi tawaye daga rundunar sojin Sudan ta SPLA.
Mr. Ban ya kuma yi fatan mahukuntan kasar Sudan ta Kudu, za su tabbatar da hukunta wadanda suka kashe ma'aikatan su 5. Kaza lika ya yi kira ga dakaru masu dauke da makamai, da su kaucewa yin duk wata barazana ga ma'aikatan jin kai.
Buga da kari babban magatakardar MDD ya yi maraba da shawarwarin da bangarorin Sudan ta Kudun ke yi yanzu haka a birnin Addis Ababan kasar Habasha, karkashin kulawar kungiyar bunkasa Gabashin Afirka ta IGAD. (Saminu Hassan)