Karkashin gangamin, a koma karatu, wanda aka kaddamar a Juba babban birnin kasar Sudan ta kudu a ranar alhamis din nan asusun da shugaban kasar ta Sudan ta kudu Salva Kiir Mayardit zasu cimma wannan manufa ga yara a jihohi 10 da suka hada da wuraren da yanzu haka suke tsaka da rikici, inji UNICEF din cikin wata sanarwa data fitar.
Kusan kashi 70 daga cikin makarantu 1,200 a manyan jihohin da rikici ya rutsa da su a rufe suke, abinda ya kawo fargaban cewa wadannan yara za'a bar su a baya saboda yakin da ake a kasar, inji Jonathan Veitch wakilin asusun a Sudan ta kudu.
Ya kara da cewa ingantaccen ilimi shine mafi muhimmanci ga cigaban kowace kasa ta fuskar tattalin arziki, walwala da al'adu. Sannan kuma yana da muhimmanci matuka ga 'yancin dan Adam.
Hargitsa karatun da rikicin kasan ya kawo ya kara lalata tsarin samar da ilimin kasar wanda da yake da rauni wanda kashi 42 a cikin 100 na yaran kasar ke samun damar shiga makarantun firamare kawai kuma kashi 10 a cikin 100 kadai ke iya kammala karatun.