Kwamitin sulhu na MDD ya fidda wata sanarwa a jiya Laraba 27 ga watan nan, inda ya yi matukar Allah wadai da harbo wani jirgin sama na tawagar musamman ta MDD a Sudan ta kudu, a ran 26 ga watan nan.
Kwamitin ya kuma nemi da lallai a gaggauta gudanar da bincike game da harbo jirgin na UNMISS tare da gurfanar da masu hannu a aikata hakan gaban kuliya ba tare da wani jinkiri ba.
A cewar sanarwar, ma'aikatan jirgin 'yan kasar Rasha 3 ne suka rasu, baya ga wani mutum guda da ya samu munanan raunuka sakamakon wannan balahira. A sa'i daya kuma, kwamitin tsaron ya bukaci da a dauki matakan da suka dace, domin tabbatar da tsaron jiragen dake zirga-zirga a sararin samaniyar kasar Sudan ta kudu.
Ya zuwa yanzu dai MDD ba ta bayyana wanda take zargi da harbo wannan jirgi ba tukuna. Koda yake a daya hannun kakakin babban magatakardar MDD Stephane Dujarric ya ce an riga an gudanar da bincike kan wannan hadari, kana Mr. Ban Ki-Moon ya yi kira ga bangarori daban-daban, da su hada kai domin ba da taimakon da ya dace. (Amina).