Kungiyar tana shiga tsakani ne don samar da zaman lafiya a kasar ta Sudan ta kudu.
Duk da cewar bangarorin biyu dake gaba da juna sun rattaba hannu akan yarjejeniya a gaban masu shiga tsakani na IGAD, saba alkawurra na ta kunno kai na ganin rikicin ya cigaba da wanzuwa. Firaministan kasar Habasha Hailemariam Desalegn wanda shi ne shugaban kungiyar ta IGAD a wajen bude taron ya ce duk da yarjejeniyar da aka cimma na kawo karshen rikicin a kuma fara shirin da zai kafa gwamnati sahihiya da za ta kawo karshen tashin hankali a kasar, wadannan alkawurra an lura ana aiwatar da sabanin hakan.(Fatimah Jibril)