Kakakin babban magatakardan MDD Stephane Dujarric ya ce wani jirgin sama, dauke da mambobin tawagar musamman ta MDD a Sudan ta kudu ya fadi a birnin Bentiu dake jihar Unity a arewacin kasar, lamarin da ya yi sanadin mutuwar ma'aikatan jirgin 3 yayin da wani guda kuma ya jikkata.
A wani taron manema labaru da aka yi a wannan rana, Stephane Dujarric ya ce jirgin saman mai saukar ungulu wanda aka yi hayar sa daga Rasha, ya yi hadari ne yayin da ya ke jigilar kayayyaki, kuma dukkanin wadanda suka rasu su 3 'yan kasar Rasha ne.
Stephane Dujarric ya kara da cewa tuni aka tura ma'aikatan rundunar zuwa wurin da hadarin ya auku, domin binciken dalilan aukuwar hadarin. (Amina)