in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Bangarorin da ke gaba da juna a Sudan ta kudu sun sanya hannu kan yarjejeniyar tsagaita bude wuta
2014-11-10 17:20:03 cri
Manzannin musamman na kungiyar IGAD da ke shiga tsakanin a rikicin kasar Sudan ta kudu, sun yi maraba da yarjejeniyar tsagaita bude wuta da gwamnatin Sudan ta kudu da bangaren adawa na SPLM suka cimma a tsakaninsu.

Kungiyar IGAD wadda ta bayyana hakan cikin wata sanarwa da aka rabawa manema labarai a ranar Lahadi ta ce, yarjejeniyar wani muhimmin mataki ne na kawo karshen yakin da ake gwabzawa a Sudan ta kudu.

Sanarwar ta kuma ce manzannin na IGAD sun yi kira ga dukkan bangarorin da su hanzarta daukar matakan da suka wajaba don aiwatar da jadawalin da aka amince ba tare da wani bata lokaci ba.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China