in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugabannin Sudan ta Kudu sun yi taro a Kenya
2015-06-30 09:49:28 cri
Shugabannin kasar Sudan ta kudu sun yi taro na sa'o'i 5 kai tsaye a Nairobi babban birnin kasar Kenya a karshen makon da ya gabata domin neman mafita a takaddamar siyasar da ta mamaye kasar mafi kuruciya a duniya.

Shugaba Uhuru Kenyatta ya ce takwaransa na Sudan ta kudu Salva Kiir Mayardit da tsohon mataimakin shugaban kasar Reik Machar sun tattauna gaba da gaba wanda ke da muhimmancin ba da kwarin gwiwwa da amincewa a tsakaninsu domin warware rashin fahimtar da juna a karshe zai samar da hanyar zaman lafiya.

Shugaba Kenyatta a cikin sanarwar da ya fitar ya ce a lokacin tattaunawar tasu na karshen mako sun gano tare da ke bi muhimman batutuwa daga dukkanin bangarori. Sun kuma tattauna sosai kai tsaye kuma shugaba Salva Kiir da tsohon Mataimakin Shugaban Reik Machar sun fahimci damuwar kowanensu da kuma uzurin junansu.

Haka kuma Shugaban kasar ta Kennya ya yi kira da shugabannin bangarorin dake arangama da juna da su bi tafarkin sulhun da yanzu haka ake kokari akai domin maido da daidaito a kasar ta Sudan ta kudu da rikici ya mamaye tun shekara ta 2013.

A lokacin tattaunawar Shugaban kasar Kenyan Uhuru Kenyatta ya ce shugabannin bangarorin na Sudan ta kudu sun bayyana cikakkaen goyon bayansu na shirin samar da zaman lafiya tare da tabbatar da nasu gudunmuwa don ganin hakan ya tabbata ga al'ummar su. (Fatimah Jibril)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China