in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kungiyar EAC ta jaddada bukatar kawo karshen rikicin Sudan ta Kudu
2015-02-21 16:58:27 cri

Kungiyar shuwagabannin kasashen gabashin Afirka ta EAC, ta bukaci daukacin sassan masu ruwa da tsaki a rikicin Sudan ta Kudu, da su gaggauta dakatar da bude wuta ba tare da wani bata lokaci ba.

EAC ta kuma bukaci bangaren gwamnati da na 'yan adawa, da su martaba yarjejeniyar wanzar da zaman lafiya da aka cimma a 'yan kwanakin baya.

Cikin wata sanarwar bayan taro da shugabannin kungiyar suka rattabawa hannu a birnin Nairobin kasar Kenya, mambobin EACn sun bayyana rungumar hanyar siyasa, a matsayin hanya daya tilo da ta dace a bi, wajen kawo karshen dauki-ba-dadin da aka kwashe watanni 14 ana gabzawa a Sudan ta Kudun.

Har wa yau EAC ta yi na'am da shawarar kafa gwamnatin hadin gwiwa ta rikon kwarya a kasar, a wani mataki na kaiwa ga cimma yanayin zaman lafiya da lumana.

A ranar 2 ga watan nan na Fabarairu ne dai bangarorin kasar Sudan ta Kudun biyu, suka amince da wata yarjejeniyar tsagaita wuta a birnin Addis Ababan kasar Habasha. Yarjejeniyar da ta tanaji dakatar da daukar dukkanin matakan soji, tare da kauracewa zub da jini tsakanin dakarun bangarorin biyu. Kaza lika an amince da sake komawa teburin shawara a ranar 19 a watan nan, gabanin babban zaman tabbatar da yarjejeniyar karshe, da aka shirya gudanarwa a ranar 5 ga watan Maris dake tafe.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China