A ranar Alhamis ne kasar Sudan ta Kudu ta gudanar da bikin murnar samun 'yancin kanta, bayan da kasar ta cika shekaru 4 da ballewa daga Sudan.
Yayin wannan biki, shugaban kasar Salva Kiir, ya yi kira da a gaggauta kawo karshen tashe-tashen hankula dake addabar sassan kasar ba tare da wani bata lokaci ba.
A cikin da ya gabatar, Salva Kiir ya nuna matukar bakin ciki game da halin da ake ciki yanzu haka a kasar, yana mai kira ga bangarori daban-daban da su koma teburin shawarwari, ta yadda za su cimma kai ga sulhuntawa, da nufin ganin kasarsu ta samu bunkasa a nan gaba.
Ban da wannan kuma, a cewarsa, yana fatan dukkanin jama'ar Sudan ta Kudu za su hada gwiwa da juna wajen kawo karshen yaki, da tabbatar da zaman karko da kwanciyar hankali cikin gaggawa.
Dadin dadawa, babban magatakardan MDD Mr Ban Ki-moon ya ba da sanarwa a ran 8 ga wata, inda ya yi kira ga shugabannin Sudan ta Kudu da su nemi wata hanya a siyasance, ta warware wannan rikici, tare kuma da cimma matsaya daya ta shimfidar zaman lafiya daga dukkanin fannoni. (Amina)