Wannan kira ya biyo bayan kammala taron koli na musamman da wakilan kungiyar ta IGAD suka gudanar karo na 27 a birnin Addis Ababan kasar Habasha, taron da firaministan kasar Habasha Haile Mariam ya jagoranta.
Kaza lika shugabannin kasashen Uganda, da Djibouti, da Sudan ta Kudu, da Kenya, da kuma mataimakin shugaban kasar Sudan Bakri Hassan Salih su ma sun kasance wakilai yayin taron.
Rahotanni dai sun ce sanarwar bayan taron da aka fitar, ta bukaci bangarori biyu da su hada kai tare da rukunin ma'aikatan bincike na kungiyar ta IGAD, don tabbatar da ma'aikatan su shiga yankin da rikici ya shafa cikin sauki, tare da sa ido ga aiwatar da manufar tsagaita bude wuta a tsakaninsu. Sanarwar ta kuma ce za a kakaba takunkumi ga duk wanda ya kawo tarnaki ga ma'aikatan rukunin.
Bugu da kari sanarwar ta yi kira ga kasashen duniya da su dauki matakan taimakawa kasar Sudan ta Kudu a kokarinta na magance tsanantar yanayin jin kai. (Zainab)