Hukumar shari'ar kasar Chadi za ta yankewa 'yan Boko Haram hukunci a bainal jama'ar, bayan tabbatar da tuhumar da ake yi musu ta shirya hare-haren bom guda biyu. Wannan ne dai karon farko da Chadi za ta yankewa 'yan Boko Haram hukunci.
Rahotanni na cewa kasancewar Chadin ba ta fitar da dokokin da suka shafi yaki da ta'addanci ba, hakan ya sa hukumar ta gabatar da karar wadannan mutane 10, bisa laifin kisan mutane ta hanyar tada bom, da mallakar makamai ba bisa ka'ida ba, da kuma gudanar da ayyukan da suka sabawa doka.
An ce wadanda ake zargin su 10, sun kaddamar da hare-haren bom biyu a birnin N'Djamena hedkwatar kasar Chadi a watan Yunin bana, lamarin da ya yi sanadin mutuwar mutane 38, yayin da kuma wasu fiye da 100 suka samu raunuka. (Amina)