Wannan gudunmuwa dai ta zo ne sakamakon yarjejeniyar hadin gwiwwa da kasashen biyu suka rattaba ma hannu a watan Oktoban bara,wanda ya kunshi horas da masana fasaha na kasar fiye da 120 a wannan bangaren na na'urar amfani da hasken rana.
Ministan Makamashi na kasar Chadi Djerassem Le-Bemadiel wanda ya karbi gudummuwar a madadain gwamnati ya ce za'a yi amfani da na'urorin a asibitocin kasar baki daya tare da gode ma kasar Sin bisa ga gudunmuwar da ya ce zai taimaka ga kau da matsalar rashin wutan lantarki sannan ya kara kulla dangantakar abota tsakanin kasashen biyu. (Fatimah Jibril)