Wannan zai kasance karo na farko da madam Amos zata je kasar Chadi tun bayan lokacin da aka nada ta a cikin watan Yulin shekarar 2010, kan matsayin karamar sakatare janar kan harkokin jin kai ta MDD kuma jami'ar dake kula da ayyukan agajin gaggawa, in ji kakakin MDD, mista Stephane Dujarric a yayin wani taron manema labarai.
Zata je can domin janyo hankalin duniya kan matsalar jin kai, musamman ma matsalar karancin abinci da rashin abinci mai gina jina da ake fama da ita, da sakamakon matsalar rikicin kasar Afrika ta Tsakiya ya janyo wa kasar Chadi dake makwabtaka da wannan kasa in ji mista Dujarric.
Zata tattaunawa ta yadda za'a sake bullo da wata mafita, domin fuskantar matsalar rashin abinci mai gina jiki dake kamari da kuma matsalar karancin abinci a yankin sahel na Chadi.
Dubun dubatar mutane suka yi gudun hijira a kasar Chadi domin gujewa tashe tashen hankali a jamhuriyyar Afrika ta Tsakiya da a halin yanzu suke bukatar taimakon gaggawa, in ji jami'an MDD. (Maman Ada)