Karfafa tsarin yin allura a dukkan fadin kasar Chadi zai taimaka wajen cimma maradun shirin kawar da cutar shan inna daga shekarar 2013 zuwa shekarar 2018, in ji mista Annour Wadak a yayin wani kamfen allurar rigakafin cutar sha inna dake gudana. Haka kuma, jami'in ya yi kira ga al'ummomin kasar baki daya da su bada hadin kai tare da yin kira ga iyaye da su kai 'ya'yansu masu watanni uku zuwa goma sha daya domin a yi musu allura. (Maman Ada)