in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Tagwayen bama-bamai sun hallaka mutane 25 a birnin N'Djamena
2015-06-15 20:25:37 cri
A kalla mutane 25 ne aka tabbatar da rasuwar su, baya ga wasu da dama da suka ji raunuka, sakamakon fashewar wasu tagwayen bama bamai, a birnin N'Djamena fadar mulkin kasar Chadi a ranar Litinin din nan.

Rahotanni daga birnin na cewa wasu mahara suka dana bama-baman, wadanda kuma ake zaton sun so ne su hallaka jami'an 'yan sanda da su.

An ce Bam na farko ya tashi ne a kusa da wani caji ofis na 'yan sanda, yayin da dayan kuma ya tashi a kusa da wata makarantar horar da 'yan sanda.

Kawo yanzu dai babu wata kafar gwamnati da ta fayyace yawan wadanda wannan hari ya hallaka. Kana wannan karon farko da babban birnin kasar Chadi ya fuskanci irin wannan hari, wanda da dama ke dangantawa da kungiyar Boko Haram.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China