Kwarewa da sanin aiki na kasar Aljeriya a hanyar kamfanin Sonatrach zai baiwa kasar Chadi damar daukaka da bunkasa arzikinta na man fetur da na gas, in ji shugaban Chadi a yayin dandalin dangantakar tattalin arziki da aka shirya albarkacin zuwan nasa a birnin Alger, in ji kamfanin dillancin labarai na APS.
Bisa wannan tunani, mista Deby ya bayyana cewa kasarsa ta shiga aikin bunkasa sha'anin man fetur dinta, tana da a yanzu wurare da dama dake kunshe da man fetur da gungun wuraren da kamfanonin kasashe dama suke aikin kansu.
Bayan man fetur karkashin kasar Chadi yana kunshe da zinari, uranium, dutse mai daraja, karfen zinc, siminti da za su iyar kasancewa wata hanyar bunkasa huldar dangantakar tattalin arziki da masana'antu tsakanin kasashen biyu.
A nasa bangare, ministan ma'adinan kasar Aljeriya, Abdesselam Bouchouareb, ya bayyana niyyar gwamnatinsa wajen rakiyar kamfanonin kasar Aljeriya wajen bude ayyukan zuba jari a kasar Chadi. (Maman Ada)