A yayin zaman majalissar dokokin na ranar Juma'a ne dai aka amince da wannan kuduri, wanda ya biyo bayan ganawar da manhukuntan Chadin suka yi, da tawagar kasar Kamaru karkashin jagorancin ministan tsaron kasar Alain Mebe Ngo'o, da kuma wata tawagar gwamnatin Najeriya.
Wata sanarwar da fadar gwamnatin kasar Kamaru ta fitar a ranar Alhamis, ta rawaito shugaba Paul Biya, na jinjinawa 'yan uwantaka da hadin gwiwa da gwamnatocin Kamaru da Chadi ke nunawa juna, musamman a fannin tabbatar da tsaro, da kokarin wanzar da zaman lafiya da lumana a kasashen.
Shugaba Biya ya ce, kamata ya yi sauran kasashen duniya su ba da nasu tallafi ga Kamaru, da ma sauran kasashen dake yankin tafkin Chadi, a kokarin da ake yi na murkushe kungiyar Boko Haram. (Saminu Hassan)