Mai magana da yawun MDD Farhan Haq ne ya bayyana hakan, ya na mai cewa hukumar kula da harkokin 'yan gudun-hijira ta MDD ta tabbatar cewa 'yan gudun-hijirar Najeriyar dake kwarara kasar Chadi, na zaune ne a wasu kauyuka masu tazarar kilomita kimanin 450 a arewa maso yammacin birni N'Djamena, tare da sauran 'yan asalin yankin.
A ranar 3 ga watan Janairun nan ne dai wani gungun 'yan bindiga da ake kyautata zaton 'yan Boko Haram ne, suka kwace garin Baga, da wasu sauran garuruwa dake arewa maso gabashin Najeriya, lamarin da ya tilasta mazauna wuraren tserewa zuwa kasashe makwabta.
Wasu rukunonin hukumar kula da harkokin 'yan gudun-hijira na MDD sun isa kan iyakar Chadi da Najeriya, inda suke kokarin tattara bayanai dangane da wadannan sabbin 'yan gudun-hijira, gami da bukatunsu.
Mista Haq ya ce, kawo yanzu adadin 'yan gudun-hijirar Najeriya dake kasar Chadi ya zarce mutum dubu 10.(Murtala)