in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sojoji a Najeriya sun gano maboyar makamai a kusa da tabkin Chadi
2014-03-16 16:02:40 cri
Rundunar sojin Najeriya dake aikin dakile 'yan tada kayar baya, ta ce ta gano wata maboyar makamai masu tarin yawa, a wani wuri dake kusa da tafkin Chadi.

Wata sanarwa daga hedkwatar tsaron kasar, wadda mai magana da yawun rundunar Manjo Janar Chris Olukolade ya sanyawa hannu a jiya Asabar, ta ce sojoji sun samu nasarar kwace maboyar makaman ne, bayan wani bata kashi da suka yi da 'yan tada kayar baya, wanda ya sabbaba rasuwar mayakan da dama.

Sanarwar ta ce ana ci gaba da jigilar makaman da aka samu daga wannan wuri.

Har wa yau a cewar sanarwar, dakarun hadin gwiwar kasashen Najeriya da Chadi na ci gaba da kaddamar da hare-hare, kan wasu karin sansanonin mayakan dake makwaftaka da tafkin na Chadi, ciki hadda Duguri, da Polkime, da kuma yankin Malafatori.(Saminu Alhassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China