Shugaban kasar Idriss Deby ne ya bayyana hakan, cikin wani jawabi da gidajen talabijin na kasar ta Chadi suka watsa a jiya Talata.
Deby wanda ya yi Allah wadai da tagwayen hare-haren bama-baman, ya bayyana aika-aikar a matsayin tsantsar rashin imani, yana mai cewa ko shakka babu wadanda suka kitsa wannan ta'asa za su hadu da fushin shari'a.
Daga nan sai ya bayyana cewa kasar sa ba za ta karaya ba, ko da kuwa wace irin barazana 'yan ta'adda za su gabatar. Ya kuma yi kira ga al'ummar Chadi da su kwantar da hankulan su, tare da kara hada kai da jami'an tsaro, wajen dakile duk wani mataki daka iya haddasa tashin hankali a kasar.