Jakadan Sin a Chadi Hu Zhiqiang ne ya rattaba hannu kan takardar mika cibiyar, shi tare da ministan kiwon lafiya na Chadi Ngariera Rimadjita wanda ya wakilci kasar sa.
Cikin jawabin sa ya yin bikin Mr. Rimadjita ya ce wannan cibiya ta horas da mata, cibiya ce irinta ta farko da aka kafa domin mata tun bayan da aka samu 'yancin kan kasar tsawon sama da shekaru 50, don haka take da muhimmanci kwarai a tarihin kasar. Ya ce a madadin gwamnatin kasar, ya na godiya ga gwamnatin Sin game da kokarin ta na sa kaimi ga bunkasar harkokin mata a Chadi, da fatan za a karfafa hadin gwiwa tsakanin kasashen biyu a fannonin kiwon lafiya, da bunkasar ayyukan zamantakewar al'umma.(Fatima)