Shugaban bikin Issouf Elli Moussami ya ce, biki na baiwa al'ummomin wurin damar mai da hankali, tare kuma cikin jituwa cikin wani shirin al'adun gargajiya da yawon bude ido dake bayyana yanayin zaman rayuwa da kuma fatansu na samun cigaba
A tsawon kwanaki biyar, makiyaya zasu hadu, kana masu yawon bude ido daga kasashen Turai zasu morewa idanunsu da abubuwa masu ban sha'awa na al'ummomin yankin Sahara ta hanyar wasannin gargajiya daban daban da suka hada da wakoki, rawa da kide kiden gargajiya, da kuma sukuwar rakuma, wata tsofuwar al'ada dake samun karbuwa tsakanin mazauna yankin Sahara da kuma gasar dafa abinci.
Haka kuma za'a gudanar da rangadin bude ido domin ganin yadda yankin Ennedi yake, a matsayin wani littafi da ke bayyana tarihin Sahara, tare da kasancewa wani zaman rayuwa inda zamani da tarihi suke cudanya.
Shugaban bikin ya ce nan da shekaru masu zuwaana fatan kafa wani gidan tarihin bikin na yankin Sahel.