Shugaban kasar Iran Hassan Rouhani ya ce Iran za ta yi iyakacin kokari kiyaye yarjejeniyar nukiliyar nan da ta daddale da kasashe shida masu ruwa da tsaki.
Mr Rouhani ya bayyana hakan ne yayin wata zantawar sa da manema labaru a daren jiya Lahadi, inda ya bayyana cewa wannan yarjejeniya za ta haifar da moriya ga bangarori daban-daban. Ya kuma kawar da damuwar da wasu 'yan kasar ta Iran ke nunawa cewa yarjejeniyar tamkar mika wuya ne ko gazawa.
Shugaba Rouhani ya ce hakan ba zai shafi tsaron asirin rundunar sojojin kasar ba, duba da cewa yarjejeniyar ta shafi batutuwa ne na hana yaduwar makaman nukiliya. Haka kuma ya ce har abada gwamnatin kasar ba za ta sadaukara da tsaro da asirin kasar ba.
Ban da haka kuma, Rouhani ya ce, bayan kawar da takunkumi dake kan kasar Iran, kasar za ta yi iyakacin kokarin bunkasa tattalin arzikinta, don kaucewa koma baya. A sa'i daya kuma kasar za ta bude kofarta ga kasashen waje don jawo jarin kasashen waje da tallafin kimiyya. (Amina)