A jiya an kaddamar da babban taron kafofin yada labaru na duniya kan yaki da ta'addanci na tsawon kwanaki biyu a birnin Damascus, inda minista Jannati ya bayyana cewa, Iran za ta ci gaba da nuna goyon baya ga Syria.
Mataimakin firaministan kasar Syria, kana ministan harkokin waje na kasar, Walid Muallem ya bayyana cewa, Syria ta yi maraba da kirar da Rasha ta yi dangane da kafa wata hadaddiyar kungiyar shiyya shiyya ta yaki da ta'addanci. A karshen watan Yunin bana, yayin da yake ganawa da mr. Muallem dake ziyara a Rasha, shugaban kasar, Vladimir Putin ya furta cewa, yanzu kungiyar IS ta fi kawo barazana a wannan yanki. Dole ne gwamnatin Syria ta yi hadin gwiwa da sauran kasashe dake wannan yanki domin yaki da kungiyar. Rasha na fatan ba da taimako wajen yin shawarwari tsakanin Syria da sauran kasashe kan wannan batu.
A gun babban taron kafofin yada labaru na duniya kan yaki da ta'addanci da gwamnatin Syria ta shirya, an yi shawarwari kan kafa hadaddiyar kungiyar shiyya shiyya ta yaki da ta'addanci, da kara saurin daidaita batun Syria a siyasance da sauransu. Wakilai daga kasashen Syria, Iran, Rasha, Masar da sauransu sun halarci wannan taro. (Fatima)