in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kwamitin sulhun MDD ya amince da yarjejeniya game da batun nukiliyar Iran
2015-07-21 10:26:41 cri
Kwamitin sulhun MDD ya zartas da wani kudurin amincewa da yarjejeniyar nukiliyar kasar Iran da aka cimma a dukkanin fannoni, wanda kuma kasashe shida da batun ya shafa da ita kanta Iran suka cimma a birnin Vienna.

Kudurin wanda aka cimma a jiya ya bayyana maraba da matsayar kasashen Sin, da Faransa, da Jamus, da Rasha, da Birtaniya, da Amurka da kuma kungiyar EU, don gane da kokarinsu tare da kasar Iran game dadaddale yarjejeniyar nukiliyar Iran din a dukkanin fannoni yadda ya kamata, inda a karshe suka cimma matsaya game da batun a ranar 14 ga watan Yulin wannan shekara.

Kana kudurin ya yi maraba da matsayin gwamnatin kasar Iran, na jaddada cewa, ba za ta nemi, ko raya, ko mallakar makaman nukiliya a ko wane irin yanayi ba, wanda hakan ke kunshe cikin yarjejeniyar da aka cimma.

Game da hakan, zaunannen wakilin kasar Sin dake MDD Liu Jieyi, ya bayyana cewa, kwamitin sulhun ya amince da yarjejeniyar, kana hakan muhimmin mataki ne na aiwatar da yarjejeniyar. Ya ce, a cikin shekaru 10 masu zuwa, yarjejeniyar za ta kasance mai matukar muhimmanci a bangaren aiwatarwa, don haka, a cewar sa, kamata ya yi bangarori daban daban su aiwatar da kudurin kwamitin sulhun, da kuma yarjejeniyar cikin adalci a dukkan fannoni. Har wa yau bisa ka'idojin girmama juna, da nuna daidaito, da kuma cimma moriyar juna, ya kamata a warware matsaloli yayin da ake aiwatar da yarjejeniyar. Ya kuma kara da cewa, Sin ta kiyaye matsayinta na sa kaimi ga cimma nasarar shawarwarin da aka kammala, za kuma ta ci gaba da sauke nauyin ba da gudummawa game da aiwatar da yarjejeniyar.

Yarjejeniya game da batun nukiliyar Iran ta hada da soke takunkumin da aka sakawa kasar Iran, da yin hadin gwiwa a fasahohin makamashin nukiliya, da sa ido ga aiwatar da yarjejeniyar, da kayyade karfin kasar Iran a fannin makamashin nukiliya da dai sauransu. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China