in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An cimma yarjejeniya game da batun nulikiyar Iran
2015-07-15 10:38:31 cri

Kasar Iran da kasashen nan shida wato Amurka, Burtaniya, Faransa, Rasha, Sin da Jamus da batun nukiliyar Iran ya shafa sun cimma wata yarjejeniya a dukkan fannoni bayan shawarwarin da suka shafe kusan tsawon wata daya suna tafkawa.

Ministan harkokin wajen kasar Iran Javad Zarif, da babbar wakiliyar EU mai kula da manufofin diplomasiya da tsaro Frederica Mogherini ne suka bayyana haka a cikin wata sanarwar da suka bayar a jiya Talata.

Wannan yarjejeniyar za ta soma aiki ne bayan da kwamitin sulhu na MDD ya zartas da kuduri kan batu a kwanaki masu zuwa. Cimma wannan yarjejeniyar ya samu yabo sosai daga kasashen duniya, amma a sa'i daya kasar Isra'ila ta nuna rashin jin dadi da cimma wannan yarjejeniya da ta kira babban kuskure da aka yi a tarihi.

A jawabin da ya gabatar ta kafar talabijin, shugaban kasar Iran Hassan Rouhani ya bayyana cewa, muddin aka zartas da yarjejeniyar yadda ya kamata, to za a kawar da rashin amincewa tsakanin kasarsa da kasashe yammacin duniya.

Shi ma babban sakataren MDD Ban Ki-moon ya bayar da sanarwar cewa, cimma wannan yarjejeniyar na bukatar a gudanar da ayyuka da dama, saboda haka ta kasance nasarar da aka samu bayan kokari da bangarori daban daban suka yi tare. Baya ga haka Ban ya bayyana imanin cewa, yarjejeniyar za ta sanya nuna fahimtar juna da hadin kai kan wasu matsalolin tsaron da ake fama da su a yankin Gabas ta Tsakiya.

A nasa bangare, shugaban kasar Amurka Barack Obama a cikin jawabinsa ya nuna yabo kan muhimmancin cimma wannan yarjejeniya a tsakanin kasar Iran da kasashen nan shida da batun nukiliyar Iran din ya shafa, kana ya bayyana cewa, an katse dukkan hanyoyin samun makaman nukiliya na Iran, ta yadda za a tabbatar da tsaron duniya.

Kungiyar EU ya bayyana cewa, za ta tsawaita sassauta takunkumin da aka sanya wa Iran har zuwa ranar 14 ga watan Janairun shekarar 2016. A wannan rana kuma majalisar kasashen Turai ta bayar da sanarwa cewa, matakin zai taimaka wa EU wajen ganin bangarori daban daban sun shirya tabbatar da aiwatar da sabuwar yarjejeniyar.

A yammacin wannan rana ne kuma firaministan kasar Isra'ila Benjamin Netanyahu ya gabatar da jawabi ta gidan talibijin, inda ya ce, cimma yarjejeniyar game da batun nukiliyar Iran da ta shafi dukkan fannoni, wani kuskure ne mai ban mamaki a tarihi, kuma duniya za ta shiga wani hadari mafi tsanani sakamakon cimma wannan yarjejeniya. (Bilkisu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China