in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban kasar Amurka ya nanata alkawarinsa na kare kasar Isra'ila
2015-07-15 13:54:15 cri

A jiya ne, shugaban kasar Amurka Barack Obama ya bugawa firaministan kasar Isra'ila Benjamin Netanyahu wayar tarho domin kawar masa da duk wani shakkun da yake da shi game da batun yarjejeniyar nukiliyar Iran da aka cimma tsakanin Iran din da kasashen nan shida da batun ya shafa, inda shugaba Obama ya yi wa Netanyahu alkawarin cewa, wannan yarjejeniyar ba za ta bar Iran ta kera makaman nukiliya ba.

Wata sanarwa da fadar shugaban Amurka ta White Housa ta bayar, ta nuna cewa, shugaba Obama ya buga waya ga firaministan kasar Isra'ila bayan da aka daddale yarjejeniyar, inda ya nanata alkawarin Amurka na kare kasar Isra'ila. Kuma yarjejeniyar za ta kau da duk wani tsoron da ake da shi na Iran kan mallakar makaman nukiliya, wadda ta kasance wani sakamakon da zai dace da muradun Amurka da Isra'ila a fannin tsaron lafiya.

Shugaba Obama ya kara da cewa, ministan tsaron kasar Amurka Ashton Carter zai kai ziyara kasar Isra'ila, matakin da ya sheda cewa, hadin gwiwar kasashen biyu a fannin tsaron ya kai wani sabon matsayi.(Kande Gao)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China