A ran 4 ga wata, bangarorin da batun ya shafa sun ci gaba da yin shawarwari a Vienna, inda suka yi karshen tattaunawa kan abubuwan dake cikin yarjejeniyar. Bisa labarin da aka bayar, an ce, ministocin harkokin wajen kasashe masu alaka da batun za su sake yin taro a Vienna domin kokarin daddale yarjejeniya ta karshe.
An labarta cewa, mai yiyuwa ne ministocin harkokin wajen za su koma Vienna a ran 5 ko ran 6 ga wata.
Jiya da safe, Mr. Yukiya Amano, babban direktan hukumar makamashin nukiliya ta kasa da kasa wanda ya koma Vienna daga kasar Iran ya hallara a yayin taron tattaunawar batun nukiliya na Iran, kuma ya fitar da wata sanarwa mai kunshe da sakamakon da ya samu a kasar Iran ga kafofin yada labaru. Mr. Yukiya Amano ya bayyana cewa, burin da yake son cimmawa a ziyararsa kasar Iran shi ne daidaita wasu matsalolin da suke shafar batun nukiliya na Iran, amma har yanzu ba a warware su ba tukuna.
Mr. Yukiya Amano ya ce, da zaran aka daddale yarjejeniyar batun nukiliya ta Iran baki daya, hukumarsa za ta aiwatar da sharudan da aka tabbatar cikin wannan yarjejeniya a kowane lokaci mai dacewa. (Sanusi Chen)