in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ya kamata bangarorin da abun ya shafa su yi kokarin daddale yarjejeniya game da batun nukiliya na kasar Iran
2015-07-14 10:33:03 cri
A safiyar jiya Litinin ne a birnin Vienna, ministan harkokin wajen kasar Sin ya gana da takwaransa na kasar Rasha Sergei Lavrov, inda ya bayyana cewa, an shiga matakin karshe game da shawarwarin nukiliyar kasar Iran, kasar Sin tana fatan yin kokari tare da Rasha don ganin bangarorin daban daban sun daddale yarjejeniya ba tare da bata lokaci ba.

A nasa bangare, Lavrov ya ce, ya yi na'am da ra'ayin kasar Sin, kuma Rasha tana fatan inganta hadin gwiwa da kasar Sin, don gaggauta an kammala shawarwarin.

Kazalika, a wannan rana, shi ma Wang Yi ya gana da takwaransa na kasar Faransa Laurent Fabius.

Inda ya ce, bayan da bangarorin daban daban suka yi shawarwari cikin amince, an samu sabon ci gaba a shawarwarin da ake kan batun nukiliyar na Iran don cimma matsaya guda tsakaninsu. Ya kamata bangarorin daban daban su yi amfani da wannan dama, don gaggauta kawo karshen shawarwarin.

A nasa bangare, Fabius ya ce, kasar Faransa ta yaba wa basirar Sin a shawarwarin, kuma Sin ta taka muhimmiyar rawa, don haka Faransa tana fatan ci gaba da shawarwari tsakanin ta da Sin game da muhimman batutuwan duniya.(Bako)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China