Yace a yanzu dai, ana cikin muhimmin lokaci ne kan shawarwari ne an kuma tsawaita lokacin shawarwari zuwa ran 7 ga wata. Kafofin yada labaru sun ba da labari cewa, kasashen shida masu kula da batun nukilyar Iran wato Amurka, Birtaniya, Faransa, Rasha, Sin da Jamus sun kusan kai ga matsaya daya da Iran kan manyan jigogi biyu wato yin bincike da saka takunkumi.
Ministan harkokin waje na kasar Sin Wang Yi a nasa bangare ya bayyana cewa, Sin na daukar matsayin cewa, ana samun zarafi mai kyau wajen daidaita batun nukiliyar Iran saboda ganin wasu muhimman abubuwa da ake da su wajen kai ga cimma wata cikakkiyar yarjejeniya a dukan fannoni. Da ya ke bayani a birnin na Vienna, Mr Wang yace batutuwa da suka rage yanzu ya kamata a warware su gaba daya, don haka ya kamata bangarori daban-daban su shirya ga yanke shawarwari a siyasance a mataki na karshe. (Amina)