Rahotanni na nuna cewa bangarorin da wannan batu ya shafa sun yi na'am da yarjejeniya kan akasarin abubuwan da ake tattaunawa, sai dai kawo yanzu ana ci gaba da tattaunawa kan batun hana kasar ta Iran cinikayyar makamai.
Yayin taron manema labaru da ya gudana a birnin Ufa da ke kasar Rasha, ministan harkokin wajen kasar Sergei Lavrov, ya ce kasar sa ta yi tayin gaggauta soke shirin hana cinikayyar makamai ga kasar Iran, duba da yadda Iran din ta tsaya tsayin daka wajen yaki da kungiyar IS. Don haka a cewar sa soke shirin hana cinikayyar makamai ga kasar zai taimakawa yakin da kasar ke yi da ta'addanci.
A jiya Alhamis, yayin da sakataren wajen Amurka John Kerry ke zantawa ta wayar tarho da takwaransa na kasar Sin Wang Yi, ya shaida masa halin da ake ciki game da batun nukiliyar Iran, yana mai yabawa muhimmiyar rawa da Sin ke takawa game da yunkurin samun nasarar shawarwarin.
Kaza lika jami'an biyu sun yi musayar ra'ayi game da matakin karshe na shawarwarin. Inda Mr. Wang ke cewa har kullum, Sin na tashi tsaye don shiga shawarwari kan batun nukiliyar Iran. Ya ce ya kuma gamsu da sabon yanayin da ake ciki game da shawarwarin dake wakana, kana Sin na fatan kara kokari tare da bangarorin da wannan batu ya shafa, wajen gaggauta daddale yarjejeniya kan batun da aka sanya gaba.(Bako)