An samu manyan ci gaba a kan wasu batutuwan da ake takkadama kansu a yayin tattauna batun nukuliyan Iran, duk da cewa har yanzu ana bukatar karin kokari domin warware wasu batutuwan da ke kan tebur. Kasashen Turai da Iran sun kusan cimma yarjejeniya kan gyara da tantance tsohon shirin makaman nukiliya da ake zargin Iran, da kuma abin da ake zaton na fadada zuwa fannin soja (PDM), da kuma babban kokarin da ya shafi tilasta mizalin karfin nukuliya na Iran an samu nasara kansu a cikin yarjejeniyar. Hukumar makamashin nukiliya ta duniya (AIEA), da ke kula da sanya ido kan nukuliya ta MDD, ta zargi Teheran da gudanar da aikin neman kera makaman nukuliya, na PMD, da sunan shirin nukuliya na jama'a, amma har kullum Iran take watsi da wannan zargi.
Iran da AIEA sun amince warware batutuwan da suka shafi PMD, amma kuma hakan na tafiyar hawainiya. Kasashen Turai sun dauki niyyar kara lokacin yarjejeniyar Geneva har zuwa ranar Litinin mai zuwa, yanzu dage wasu takunkumi da aka kakabawa Teheran, da yin kokarin diplomasiyya na karshe domin warware batun nukuliyan Iran mai sarkakiya. Tilasta misalin karfin nukuliyan Iran a cikin yarjejeniyar, da ke kasancewa wani babban ci gaba, na nuna cewa za a iya cikin dan lokaci ga kai a cikin manufar binciken Iran tare da wasu na'urorin tantance masu ci gaban gaske. (Maman Ada)