in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ministan harkokin wajen Sin ya gana da takwaransa na kasar Birtaniya
2015-07-07 14:01:04 cri

A yammacin jiya Litinin 6 ga wata, a birnin Vienna, ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi da ke halartar shawarwari kan batun nukiliya na kasar Iran don daddale yarjejeniya daga duk fannoni, ya gana da takwaransa na kasar Birtaniya Philip Hammond, inda bangarorin biyu suka yi musayar ra'ayi game da dangantakar dake tsakanin kasashen Sin da Birtaniya da batun nukiliya na kasar Iran.

A nashi bangaren Mr Hammond ya ce, Birtaniya na jiran ganin ziyarar da shugaban kasar Sin Xi Jinping zai kai a kasar,domin ta yi imani cewa, ziyarar za ta haifar da babban tasiri game da alakar bangarorin biyu.

Ya kuma bayyana ra'ayinsa dangane da shawarwari kan batun nukiliyar kasar Iran cewa, ya kamata bangarorin da abun ya shafa su yi amfani da wannan dama, don warware matsaloli, domin ta hakan ne za a samu nasarar shawarwari.

Shi kuma a nasa bangare, Wang Yi ya ce, kasar Sin na fatan inganta hadin gwiwa da Birtaniya, don zage damtse game da wannan ziyara ta kafa tarihi da shugaban kasar Sin zai kai Birtaniya, don tabbatar da wannan ziyara cikin nasara.

Game da batun nukiliya na kasar Iran, Wang Yi ya ce, an shiga mataki na karshe don daddale yarjejeniya kan batun nukiliya na kasar Iran, yanzu ya kamata a yi kaunar nasarorin da aka samu. Ya zama dole kasashe 6 da batun nukiliya na Iran ya shafa su yi kokari tare da Iran, don yanke shawara, ta hakan, za a samu cimma daidaito a cikin shawarwari.(Bako)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China