Wannan dai mataki ya kawo karshen rashin amincewar da aka samu a baya, an kuma daidaita wannan matsala ta Iran a siyasance bayan shafe tsawon shekaru 13 ana fama da shi.
Wannan yarjejeniya dai ta shafi batun kakaba takunkumi, da batun nukiliya, da shiga tsakanin kasashen shida, da hadadden kwamitin Iran, da hadin gwiwa a fannin makamashin nukiliya, da kuma shirin gudanar da yarjejeniyar.
Abubuwan dake cikin yarjejeniyar dai sun hada dukkanin muhimman fannonin dake shafar aikin daidaita batun nukiliyar kasar ta Iran. Dadin dadawa, bayanan da aka cimma matsaya a kan su yayin wannan karo sun hada da wani daftarin kudurin kwamitin sulhu na MDD.
Bisa yarjejeniyar, za a soke, ko dage yawancin takunkumin da kwamitin sulhun MDD, da Amurka, da kuma kungiyar EU suka kakaba wa Iran sakamakon shirinta na nukiliya. A sa'i daya kuma, dole ne Iran ta cika alkawuran da ta dauka na kayyade shirinta na nukiliya, da kuma yin amfani da shi domin tabbatar da zaman lafiya, tare da amincewa gamayyar kasa da kasa su sa mata ido a fannin shirin ta na sarrafa nukiliya.
Wannan yarjejeniya da daftarin kudurin za su fara aiki ne bayan da aka mika su ga kwamitin sulhun MDD domin tattaunawa tare da zartas da su. Daga bisani, bangarorin daban daban za su shafe wasu watanni suna share fagenn gudanar da yarjejeniyar yadda ya kamata.(Fatima)