Sanarwar ta ce, lamarin ya auku ne da misali karfe 3 na yammacin ranar Asabar, lokacin da sojojin kasar ke fafarar wasu masu laifi, tare da kwace wasu makamai daga hannunsu. Koda yake ba a yi cikakken bayanin asalin su ba tukuna.
Sanarwar da gwamnatin ta bayar, ta kuma yi kakkausar suka game da harin wanda aka bayyana da danyen aikin rashin imani. A cewar sanarwar irin wannan aiki zai kawo cikas ga kokarin da ake yi na shimfida zaman lafiya a kasar.
Rahotanni na nuna karuwar hare-hare a arewacin kasar Mali. Duk kuwa da cewa gwamnatin kasar ta daddale yarjejeniyar wanzar da zaman lafiya da wakilan wasu daga dankarun dake birnin Bamako fadar mulkin kasar, da na arewacin kasar a ranar 15 ga watan Mayun da ya shude. Sai dai koda a wancan lokaci manyan sassa uku na kungiyar CMA ba su sa hannu kan yarjejeniyar tsagaita wutar ba.
A kuma ranar 20 ga watan Yuni, CMA ta rattaba hannu kan wannan yarjejeniyar, matakin da ya alamanta cewa daukacin bangarori dake da nasaba da lamarin sun amince da wannan yarjejeniya. (Amina)