in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ban Ki Moon ya yi maraba da sanya hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya a Mali
2015-05-16 16:19:15 cri
Babban magatakardar MDD Ban Ki Moon, ya yi maraba da sanya hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya, tsakanin gwamnatin Mali da wasu kungiyoyin 'yan tawayen kasar.

Da yake tsokaci game da hakan, Mr. Ban ya ce yarjejeniyar ta kasance muhimmin mataki, a shirin da ake yi na wanzar da zaman lafiya a arewacin kasar ta Mali. Ya kuma yi fatan daukacin sassan da suka amince da wannan yarjejeniya za su mutunta nauyin da suka dauka.

Har wa yau babban magatakardar MDDr ya yi fatan cewa sauran kungiyoyin da ba su shiga yarjejeniyar ba za su gaggauta mika wuya, ta yadda za a ci gaba da gudanar da shawarwari cikin hadin gwiwa, duka dai da nufin cimma nasarar da aka sanya gaba.

A ranar Jumma'a ne dai wakilan gwamnatin kasar ta Mali suka amince da wannan yarjejeniya ta sulhu, tsakaninsu da wakilan gamayyar wasu daga kungiyoyin 'yan adawar kasar, ko da yake kungiyar 'yan a ware ta Azbina ko CMA, ba ta shiga yarjejeniyar ba. (Saminu Hassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China