Wata majiya ta shaidawa kamafanin dillancin labarum kasar Sin Xinhua cewa, cikin wadanda aka kame hadda 'yan kasar ta Mali, da 'yan Mauritania. An kuma ce sun tsallaka cikin kasar ne daga Cote d'Ivoire a ranar Litinin. Tuni dai aka garzaya da su zuwa babban birnin kasar Bamako.
Wannan dai lamari na zuwa ne 'yan kwanaki, bayan da jami'an tsaron kasar suka cafke wasu 'yan ta'addar na daban, cikin su hadda daya dauke da takardun farfaganda, na kungiyar Ansar Dine ta masu Jihadi, kungiyar da a baya bayan nan ta dauki alhakin kai hare-hare kan rundunar sojojin kasar, da dakarun tawagar wanzar da zaman lafiya dake kasar, a yankunan arewaci da kuma kudancin kasar.(Saminu Alhassan)