Kwamitin sulhu na MDD ya ba da wata sanarwa a ran 10 ga wata, domin kalubalantar wata kungiyar adawa da gwamnati dake arewacin kasar da ake kira CMA da ta sa hannu kan yarjejeniyar shimfida zaman lafiya.
Sanarwar ta ce, kwamitin na maraba da yarjejeniyar wanzar da zaman lafiya da gwamnatin Mali ta daddale tare da wasu kungiyoyi masu adawa da ita dake arewacin kasar a ranar 1 ga wata Maris da ya gabata a birnin Algiers hedkwatar kasar Aljeria. A ganin kwamitin sulhun, yarjejeniyar ta shafi fannoni daban daban, wadda ke da zummar warware matsalolin Mali,ta fuskokin siyasa, tsaro, bunkasuwa da dai sauransu.
An ba da labari cewa, kungiyoyi masu adawa da gwamnati guda shida sun kulla wannan yajejeniya da gwamnatin kasar Mali a ran 1 ga watan Maris, amma kungiyar CMA a matsayin babbar kungiyar dakaru ta kabilar Abzinawa ta kauracewa sanya hannu kan wannan yarjejeniya bisa dalilin cewa akwai bukatar sake nazarin abubuwan dake cikin yarjejeniyar. (Amina)