A cikin jawabin da Mr,Osler,wani babban jami'in kungiyar wanzar da zaman lafiya da M.D.D. ta tura Mali MINUSMA ya bayar, an ce, sojojin kiyaye zaman lafiya na Sin sun taka muhimmiyar rawa a yunkurin samar da zaman lafiya a kasar Mali. Sojojin Sin sun yi ayyuka tukuru a fannoni daban daban, wanda ya zama wani abin koyi ga kungiyarsa ta MINUSMA.
Jakadar Sin da ke kasar Mali Lu Huiying ta jinjina wa muhimmiyar rawa da sojojin kiyaye zaman lafiya na Sin suke takawa wajen shimfida zaman lafiya, da sa kaimi ga sada zumunci tsakanin kasashen Sin da Mali. Ta ce, an mika wannan lambar yabo ba ma kawai ga sojoji din ba, har ma ga kasar Sin da ta tashi tsaye don taimakawa kasar.
Rukunin sojojin kiyaye zaman lafiya da Sin ta tura Mali a karo na 2 ya kunshi injiniya 155, da 'yan sanda 170, har ma da likitoci 70, wadanda ke gudanar da ayyukan gine-gine, tsaro, kiwon lafiya da bada hidimar jinya.(Bako)