in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ban Ki-moon ya nuna maraba da yarjejeniyar zaman lafiya a Mali
2015-06-21 13:53:47 cri
Jiya Asabar 20 ga wata, babban magatakardan MDD ya fidda wata sanarwa ta bakin kakakinsa, inda ya nuna cewa, yana maraba da babbar kungiyar adawa da gwamnatin kasar Mali ta CMA da ta sanya hannu kan yarjejeniyar neman sulhu da zaman lafiya a babban birnin kasar, Bamako a wannan rana.

Cikin sanarwar, Ban Ki-moon ya taya wa bangarorin kasar Mali da abin ya shafa murnar cimma yarjejeniyar neman sulhu, ya kuma bayyana cewa, bayan da aka cimma yarjejeniyar, za a iya gudanar da harkokin neman sulhu a kasar Mali bisa dukkanin fannoni.

Kaza lika, Ban Ki-moon ya sake jaddada cewa, MDD za ta goyi bayan kasar Mali wajen gudanar da harkokin yarjejeniyar neman sulhu, a sa'i daya kuma, za ta yi hadin gwiwa tare da gwamnatin kasar Mali da kuma kungiyoyin shiga tsakani na duniya kan wannan aiki. Kana, ya kuma sa kaimi ga bangarorin da abin ya shafa da su nuna goyon baya kan aiwatar da yarjejeniyar yadda ya kamata, domin taimaka wa kasar Mali wajen shimfida zaman lafiya na dindindin.

A ran 20 ga wata, a gaban idanun shugaban kasar Mali Ibrahim Boubacar Keita da kuma wakilin musamman na babban magatakardan MDD dake kula da batun kasar Mali Mongi Hamdi, babban wakilin kungiyar adawa da gwamnatin kasar Mali ta CMA aka sanya hannu kan yarjejeniyar neman sulhu da zaman lafiya, lamarin da ya nuna cewa, an cimma nasarar kulla yarjejeniyar zaman lafiya a kasar Mali.

A ran 15 ga watan Mayu, gwamnatin kasar Mali da wasu wakilan kungiyoyin adawa da gwamnatin dake arewacin kasar sun kulla yarjejeniyar zaman lafiya, amma babbar kungiyar adawa dake arewacin kasar ta CMA ba ta halarci bikin sanya hannu ba. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China