in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An kai hari ga wata motar ICRC a kasar Mali
2015-03-31 10:40:47 cri
An kai hari ga wata babbar motar daukar kaya ta kwamitin kasa da kasa na ba da agaji na the Red Cross wato ICRC a arewacin kasar Mali a ranar litininLitinin, wanda ya haddasa mutuwar mutum daya, yayin da kuma mutum dayawani ya ji rauni.

Bisa sanarwar da kwamitin bayar da agajinICRC ya bayar, an ce, mutumin da ya mutu a sakamakon hari shi ne direban motar kuma ma'aikacin kwamitin ICRC. An kai harinHarin ya faru ne yayin da yake tuki daga birnin Gao dake arewacin kasar Mali zuwa birnin Niamey, babban birnin kasar Nijer don yin jigilar kayayyakin kiwon lafiyaagaji na da asibitin Gao ke bukata. Mutumin da ya ji rauni kuma shi ne dan kasar Mali dake aiki a kwamitin ICRC, ya zuwa yanzu, bai fuskantar hadarin rasa rayuka ba.

Sanarwar ta yi nuni da cewa, ba a san dalilin da ya kawo wannan hari ba.

Duk da hakan Kwamitin ICRC ya yi Allah wadai da harin, kana ya yi kira ga bangarori daban daban na arewacin kasar Mali da rikici ya shafa da su tabbatar da tsaron fararen hula da girmama ayyukan kwamitin ICRC. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China