Rundunar kiyaye zaman lafiya ta kasar Sin zagaye na uku dake kasar Mali, karo na farko ke nan da ta yi amfani da wata sabuwar na'urar da Sin ta kera, wadda ke iya hana fashewar bam cikin wata da'irar mai tsawo kimanin mita 100, bisa fasahar katsalandan na'urorin tada boma-bomai.
An ba da labari cewa, halin da Mali ke ciki na kara tsananta a kwanakin nan, yankin Gao na fama da hare-haren rokoki da boma-bomai da ake kaiwa rundunar kiyaye zaman lafiya da ke wajen.
Babban hafsan mai ba da umurni na rundunar a wannan karo Tian Wei ya ce, wannan sabuwar na'ura na da amfani wajen baiwa sojojin kiyaye zaman lafiya kariya lokacin da suke kai sintiri. (Amina)