Cikin sanarwar, kwamitin ya kuma bayyana cewa barkewar rikice-rikice a yankin Gao dake arewacin kasar ta Mali, tun daga ranar 27 ga watan Afrilun da ya gabata, ya sabawa yarjejeniyar tsagaita bude wuta da aka sanyawa hannu a baya.
Kana kwamitin sulhu ya nuna goyon baya ga matakan da sojojin kiyaye zaman lafiya na MDD ke dauka, don sassauta yanayin da ake fuskanta a kasar ta Mali, da kuma kokarinsu, wajen ciyar da shawarwari tsakanin bangarorin daban daban gaba. Bugu da kari, kwamitin na sa kaimi ga bangarorin daban daban na kasar da su ci gaba da halartar zaman shawarwari, domin cimma nasarar kulla daftari na yarjejeniyar zaman lafiya a birnin Bamako, fadar mulkin kasar, wanda ake sa ran gudanar a ranar 15 ga watan nan na Mayu. (Maryam)