Daga cikin wadannan ayyuka na tashin hankali akwai kisan mutane ba ji ba gani kuma ba bisa doka ba, cafke mutane da tsare su gidan yari ba bisa doka ba, azabatarwa, amfani da kananan yara cikin aikin soja daga wajen kungiyoyin masu makamai, kwace dukiyoyin jama'a da lalata kayayyaki, a cewar wannan rahoto na farko na hadin gwiwa tsakanin tawagar MINUSMA dake kasar Mali da babbar hukumar kare 'yancin dan Adam ta MDD (HCDH).
Wajibi ne tashe tashen hankali da munanan ayyukan keta hakkin dan adam da na 'yancin jin kai da aka aikata a kasar Mali su kasance ayyukan da aka yi bincike mai zurfi kuma cikin adalci, wannan kuma domin martaba mutanen da abubuwan shuka shafa da sassanta al'ummomin kasar Mali, in ji wakilin musammun na sakatare janar na MDD da ke kasar Mali, Mongi Hamdi.
MDD za ta ci gaba da kawo tallafin da ya dace ga hukumomin kasar Mali domin tabbatar da cewa an karfafa ayyukan bunkasa da kare 'yancin dan adam a kasar Mali, in ji mista Hamdi. (Maman Ada)