Rahotanni na cewa, tawagar sojojin tana kunshe ne da mutane guda 395, wadanda suka hada da kananan tawagogi guda uku na 'yan sanda, sojojin injiniya da na ba da jinya, wadanda aka tura zuwa yankin Gao na kasar Mali.
Bugu da kari, gabanin su fara wannan aiki na kiyaye zaman lafiya, wadannan kanannan tawagogi guda uku suka fara samun horo a asirce, sa'an nan kuma, sojojin za su kara fahimtar dokoki, al'adu da kuma harkokin addinin kasar Mali, wannan zai taimaka musu wajen tabbatar da kammala ayyukansu cikin nasara. (Maryam)