Kungiyar ta fitar, an ce, babban makasudin harin din da kungiyar ta shirya shi ne kai farmaki ga rundunar sojan kasar Nijer ta tawagar sulhu ta musamman da MDD ta tura zuwa kasar Mali, kana kungiyar ta shirya harin domin nuna kiyayya ga kasashen Faransa da Amurka da su kafa sansanonin soja a kasar Mali, da kuma halartar shugaban kasar Nijer taron gangami kan mujallar Charlie domin nuna goyon baya ga kasar Faransa.
A ran 15 ga wata, wata mota dake daukar boma-bomai ta shiga sansanin tawagar sulhu ta musamman ta MDD a garin Ansongo dake yankin Gao, inda boma boman suka tashi, lamarin da ya haddasa mutuwar fararen hula guda uku, yayin da 16 suka jikkata, ciki har da da sojojin kiyaye zaman lafiyar kasar Nijer guda 9. (Maryam)