Mr. Ban wanda ya bayyana hakan ta bakin kakakin MDD Stephane Dujarric, ya ce ya zama wajibi a dauki matakan warware matsalar Arewacin kasar ta Mali bisa dabaru na siyasa. Wannan dai tsokaci na Ban Ki Moon na zuwa ne kwanaki 2, bayan aukuwar wani hari da ya raunata wasu jami'an tawagar MINUSMA su 7, sakamakon wata nakiya da motar da suke ciki ta taka a yankin Kidal.
Daga makon da ya gabata zuwa yanzu, hare-haren da ake shiryawa a wannan yanki sun yi sanadiyar rasuwar fararen hula 5, da jikkatar wasu 13, baya ga jami'an wanzar da zaman lafiyar MDDr su 16 da hare-haren suka raunata.
Kwamitin tsaron MDD ne dai ya kafa tawagar MINUSMA cikin shekarar 2013, tawagar da aka dorawa alhakin tallafawa shirin dawo da tsarin dimokaradiyya a kasar, tare kuma da baiwa harkokin tsaro tallafin da ya wajaba.