in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kungiyar Taliban ta nada sabon shugabanta
2015-08-01 14:18:13 cri

Kungiyar Taliban ta Afghanistan ta ba da wata sanarwa a daren Jumma'a ran 31 ga watan Yuli, inda da ta sanar da Mullah Akhtar Mohammad Mansoor a matsayin sabon shugabanta.

A cikin wannan sanarwa, an bayyana Mansoor a matsayin babban abokin aiki na Zumun Mullah Mohammad Omar (tsohon shugaban kungiyar) ", wanda shi ya kasance tsohon mai ba da taimako ga Omar. Kafar yada labaru ta kasar ta ba da labarin cewa, Mansoor ya taba rike mukami a cikin gwamnatin Taliban, kuma a shekarar 2013 dai, ya zama wanda ya rike shugabancin Taliban duk da cewa bai kai mukamin shugaban kungiyar ba.

An ba da labari cewa, a daren ran 30 ga watan Yuli, Kungiyar Taliban ta tabbatar da cewa, shugabanta Mullah Mohammad Omar ya rasu sakamakon rashin lafiyar jikinsa, amma hukumar tsaron kasar Afghanistan ta sami shaidun dake tabbatar da cewa, Omar ya mutu tun kafin shekarar 2013 a wani asibitin kasar Pakistan. (Amina)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China