A wannan rana, mista Obama ya gana da shugaban kasar Afghanistan Ashraf Ghani Ahmadzai a fadar White House, kuma wannan shi ne karo na farko da shugaba Ahmazai ya kai ziyara a kasar Amurka, bayan da ya hau kan karakar mulkin kasa a shekarar da ta wuce. Bayan ganawarsu, shugaba Obama ya bayyana a yayin taron manema labarai cewa, bayan shawarwarin da ya yi tare da manyan jami'an tsaro, ya tsai da kudurin rike adadin sojojin kasarsa a kasar Afghanistan har zuwa karshen shekarar bana, kuma zai tsara saurin janye sojojin kasar daga Afghanistan na shekara mai zuwa a karshen shekarar bana.
A nasa bangaren kuma, Ashraf Ghani Ahmadzai ya bayyana cewa, rage jinkirta saurin janye sojojin kasar Amurka daga kasarsa zai taimaka wa kasar Afghanistan wajen gaggauta yunkurin yin kwaskwarima, kuma lamarin zai ba da tabbaci ga sojojin tsaron kasar Afghanistan wajen samun karin goyon baya a fannonin jagoranci, kayayyakin sojoji da kuma horaswa. (Maryam)